Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tagwayen Harin Kunar Bakin Wake A Kabul Ya Kashe Mutane 22


Jami’an kasar Afghanistan sun ce wasu tagwayen harin kunar bakin wake a Kabul, babban birni kasar ya kashe akalla mutane 22, wasu su 70 kuma sun jikkata.

Wadanda suka shaida lamarin sun ce ‘yan bindigan sun auna wata tawagar jami’ai da suka bar ofisoshin majalissar kasar ne. Ta yiwu adadin wadanda suka rasu ya karu.


Manyan jami’an tsaro da fararen hula, da wasu ma’aikatan majalissar kasar na cikin wadanda abin ya shafa.


Rahotannin farko sun ce wani dan kunar bakin wake ne ya tarwatsa kansa kusa da ofisoshin majalissar a unguwar Darulama dake birnin, jim kadan kafin wani maharin ya tada nakiyoyin dake dankare a motarsa.

XS
SM
MD
LG