Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Mijin Dora Akunyili


'Yan Bindiga.
'Yan Bindiga.

Rahotanni sun bayyana cewa an kashe Dr. Akunyili ne da yammacin ranar Talata, a Umuoji da ke yankin karamar hukumar mulki ta Idemili ta Arewa a jihar Anambra.

Wasu ‘yan bindiga da ba'a tantance ko su waye ba sun harbe Dr. Chike Akunyili, mijin tsohuwar ministar watsa labarai kuma tsohuwar shugabar hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya, Farfesa Dora Akunyili.

Rahotanni sun bayyana cewa an kashe Dr. Akunyili ne da yammacin ranar Talata, a Umuoji da ke yankin karamar hukumar mulki ta Idemili ta Arewa a jihar Anambra.

Dr. Chike Akunyili
Dr. Chike Akunyili

Lamarin ya auku ne a yayin da ya ke kan hanyar dawowa daga halartar wani taron lacca a birnin Onicha, da kungiyar tsofaffin daliban jami’ar Najeriya ta Nsukka ta shirya domin karrama matarsa Dora Akunyili.

Lamarin ya haifar da martanoni daban-daban daga masu fashin baki, wadanda akasari suke ta’allaka hakan da karuwar tabarbarewar lamurran tsaro a Najeriya.

XS
SM
MD
LG