Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Mutane 11 A Wani Yunkurin Fashi a Tafawa Balewa, Jihar Bauchi


Hoton wani da harin bama-bamai a Kano ya rutsa da shi yake kwance a sibiti.

Rundunar ‘Yan sanda ta jihar Bauchi ta tabbatar da an kashe akalla mutane 11 sakamakon wani yunkurin fashin da aka so yi kan wani banki cikin daren jiya a garin Tafawa Balewa.

Rundunar ‘Yan sanda ta jihar Bauchi ta tabbatar da an kashe akalla mutane 11 sakamakon wani yunkurin fashin da aka so yi kan wani banki cikin daren jiya a garin Tafawa Balewa.

Kwamishinan ‘Yansanda na jihar Ikechukcwu Aduba ne ya tabbatar da haka, a wani taron manema labarai.yace tuni rundunar ta damke mutane shida dangane da wan nan yukurin fashin.

Ahalinda ake ciki kuma, wasu nakiyoyi sun tashi a cikin wasu majami'u cikin birnin Bauchi. Sabo da karfin fashewar da farko mutane sun aza bama-bamai ne. Amma 'Yan Sanda sun hakikance cewa irin nakiyoyin da ake fasa duwatsu dasu ne suka tashi a coci-cocin.

Fshe fashen da suka auku da misalin karfe 3 na asubahin lahadi sun huda rufin kan dakin ginin cocin da lalata tagoginsu.

Saurari:

Aika Sharhinka

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG