Accessibility links

An kashe mutane 16 a wani artabu tsakanin jami'an tsaron da kungiyar mayaka a Najeriya


Wani harin kunar bakin wake da mayaka suka kai

Jami'an tsaro sun ce wata musayar wuta da aka yi da mayakan kishin Islama tayi sanadin mutuwar mutane 16.

Ma;iaktun tsaro a Nigeria sunce wani gumurzu da aka tapka tsakaninsu da ‘yan kungiyar kishin Islama a Maiduguri, fadar jihar Borno dake arewa-maso-gabashin kasar ya sa 16 daga cikin ‘yan kishin Islama din sun rasa rayukkansu.

Kwamnadan rundunar hadin gwaiwa ta J-T-F a can Maiduguri, Col. Victor Ebhaleme yace wannan tashin hankalin ya faru ne a unguwanni Lawan Boukar da Shehuri masu yawan jama’a dake birnin.

Yace sojan na Nigeria sun kwato makamai da albarussai da yawa daga wa’anda suka cafke, kuma sun bata wasu daga cikin bama-bamman da suka samu a wurraren.

Maiduguri dai itace kamar hedkwatar kungiyar ‘yan Boko Haram dake son girka shari’a a Nigeria, wacce kuma take cewa ita sam bata yarda da hallacin gwamnatin tarayya da kuma kundin tsarin mulkin kasar ba.

Kungiyar ce ta dauki alhakin mummunan farmakin da aka kai na kunar bakin wake ranar Lahadi akan wata coci dake garin Bauchi inda har mutane 15 suka rasa rayukkansu. Boko Haram ta sha kai irin wadannan hare-haren akan majami’u, ciki harda wanda ta kai Abuja a Kirsemetin da ta wuce, inda mutane fiyeda 30 suka rasa rayukkansu.

Ra’ayinka

Show comments

XS
SM
MD
LG