Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Mutane Akalla 70 A Arewacin Najeriya


Wadanda suka ji rauni da kuma gawarwaki lokacin tashin wani bam a garin Kaduna, a ranar alhamis 26 Afrilu, 2012.

Jami'ai sun ce mutanen da suka mutu cikin kwanaki ukun da suka shige a Kaduna da Damaturu da Zariya ya zarce saba'in

An kashe mutane akalla saba’in cikin kwanaki ukun da suka shige a wasu garuruwa biyu na Najeriya, a tashe-tashen hankulan da suka biyo bayan hari kan wasu majami’u.

Hare-haren bam na kunar-bakin wake kan majami’u a garuruwan Kaduna da Zariya sun kashe mutane fiye da 20, suka haddasa hare-haren ramuwar gayya na gungu-gungun Kiristoci. Jami’ai sun ce an kashe mutane 52, yayin da wasu fiye da 100 suka ji rauni a wannan tashin hankali a Jihar Kaduna.

A ranar litinin, tashin hankali ya kuma barke a garin Damaturu, inda aka samu rahoton kashe mutane fiye da 20. Shaidu sun ce ‘ya’yan kungiyar Boko Haram sun kai hare-hare da bindigogi a wurare da dama na garin. ‘Yan sanda sun fadawa Muryar Amurka jiya talata cewa an kashe jami’an tsaro akalla uku a wannan lamarin.

Jami’ai a Jihar Kaduna sun ce mutane sun bazu kan tituna jiya talata su na zanga-zanga da kone-kone. Kwamishinan yada labarai na Jihar Kaduna, Saidu Adamu, ya fadawa Muryar Amurka cewa hukumomi su na dora laifin wannan fitina a kan Kiristoci da Musulmi.

Wannan tashin hankali ya sa hukumomi a Damaturu da Kaduna sun kafa dokokin hana fita na duk tsawon rana da dare.

Tashin hankali ya karu cikin ‘yan makonnin nan a arewacin Najeriya, abinda ya haddasa fargabar barkewar mummunar fitinar bambancin addini a fadin yankin.

XS
SM
MD
LG