Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Mutumin Da Ake Zargi Da Kitsa Harin Spain


Dandazon mutanen da suka taru a wurin da aka kai hari a birnin Barcelona domin nuna alhininsu

Hukumomin kasar Spain ko kuma Andalus, sun bayyana cewa sun kashe madugun da ya jagoranci harin motar da ya kai ga mutuwar mutane sama da goma a kasar a ranar Alhamis.

Kafofin yada labaran kasar Spain, sun ce an kashe mutumin da ake zargi da kitsa harin da aka kai kasar, mai suna Moussa Oukabir, bayan wata musayar wuta da suka yi da ‘yan sandan kasar.

Rahotannin sun ce Oukabir, na daya daga cikin mutane biyar da aka kashe wadanda duk ake zargi da kai harin garin Cambrils dake bakin gabar teku, sa’oi bayan da wata mota ta kutsa cikin mutane a birnin Barcelona a ranar Alhamis, inda mutane 13 suka rasa rayukansu.

Wani jami’in tsaro a kasar ta Spain, ya fadawa kamfanin dillancin labaran Associated Press cewa Oukabir, wanda shi ake zargi da tuka motar, na daya daga cikin mutane biyar da aka harbe har lahira a garin na Cambrils.

Facebook Forum

Bidiyo

Yadda Wani Mutum Ya Mari Shugaban Faransa Emmanuel Macron
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:37 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Marigayi TB Joshua
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Gidajen Rediyon Najeriya Sun Gana Da Jami'an Diplomasiyya Kan Rikicin Twitter
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:51 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG