Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Sama Da Mutum 60 a Wani Hari a Sudan


Rahotannin sun ce an kashe sama da mutum 60 kana kusan wasu su 60 sun jikkata a ranar Asabar a lokacin wani harin makamai a wani kauye da ke yankin Dafur a Sudan wanda ke yawan fuskantar tashin hankali, a cewar hukumar kula da ayyukan jinkai ta Majalisar Dinkin Duniya da yammacin ranar Lahadi 26 ga watan Yuli.

Harin na kauyen Masteri da ke yammacin jihar Darfur "shine na baya-baya a cikin jerin matsalolin tsaro da aka sanar a makon da ya gabata wanda ya yi sanadiyyar kona kauyuka da gidaje da yawa, kana aka wawushe dukiyoyi a kasuwanni da shaguna, aka kuma lalata gine-gine, a cewar sanarwar hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya. Sai dai hukumar ba ta yi wani karin bayani a kan majiyarta ba.

Ya zuwa yazu babu wani bayani a hukumance daga gwamnatin kasar a kan harin, kuma kamfanin dillancin labaran Reuters bai samu damar tuntubuar jami’ai domin karin bayani ba.

A ranar Lahadi, Sudan ta ce za ta jibge rundunar tsaron hadin gwiwa daga jihohi da yawa a Darfur biyo bayan sake kunnowar tashin hankalin kwanan nan a wurin, a cewar SUNA, kafar yada labaran kasar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG