Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Shugaban Kasuwar Shanu a Bayelsa


Kasuwar Shanu

Wasu yan bindiga da ba a gano su ba, sun kashe shugaban kasuwar shanu a Bayelsa Alhaji Jibril Abdulkarin da wasu mutane uku yayin da suke wata ganawa. Yan bindigan sun kai wannan harin ne a Azikoro Road a garin Yenagoa a cikin jihar Bayelsa.

Wannan harin ya haifar da zaman dar-dar tsakanin al’ummar Arewa dake zaune a jihar ta Bayelsa wadanda suka nemi kariyar jami’an tsaro. Wannan al’amrin ya kuma ya kai ga suka rufe hanyoyin mota domin bayyana damuwarsu ga harin.

Hukumomin tsaro a jihar Bayelsa sun yi alkawari ga al’ummar Arewacin Najeriya dake zaune a jihar cewa za a basu tsaro da dukiyoyinsu. A cewar wani makarabin wadanda aka kaiwa harin, sakataren gwamnatin jihar Bayelsa yace musu kada wani Bauhashe ya ji tsoron gudanar da harkokinsa saboda za a basu cikakken tsaro.

Mai Magana da yawun yan sandan jihar DSP Andrew Busuwad ya bayyana yanda maharan suka kai farmaki a cikin wata mota kirar Mazda. Sai dai yace tuni ma’aikatar yan sandan jihar ta umarci jami’anta su nemi motar su kama ta.

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:03:33 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG