Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Shugaban Kungiyar Al-Shabab, Ahmed Abdi Godane


Ahmed Abdi Godane

An kashe shugaban kungiyar Al-Shabab, Ahmed Abdi Godane.

Jami’an gwamnatin Amurka sun ce sun samu tabbacin cewa wani harin da aka kai ta sama a kasar Somaliya ya kashe shugaban kungiyar al-Shabab, Ahmed Abdi Godane.

Sakataren yada labarai na ma’aikatar harkokin wajen Amurka, Rear Admiral John Kirby, yace wani matakin sojan da Amurka ta dauka a kan Godane ranar litinin, shi ne ya zamo ajalinsa.

Shaidu sun bayarda rahoton cewa wani jirgin saman yaki maras matuki na Amurka, ya cilla makamai masu linzami a kan wani taron shugabannin kungiyar al-Shabab a kudancin Somaliya.

Wata sanarwar fadar White House ta fada a yau jumma’a cewa kawar da Godane daga bakin daga, Wata babbar hasara ce ga kawar al-Qa’ida mafi girma a nahiyar Afirka, kuma ya biyo bayan ayyukan leken asiri da na soja da aka shafe shekara da shekaru ana yi.

XS
SM
MD
LG