Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Sojojin Amurka Biyu A Jamhuriyar Niger.


Amurka ta bada tabbacin mutuwar sojojin ta biyu dake aikin samar da tsaro a Jamhuriyar Nige,Sai dai ba wanda ya dauki alhakin aikata wannan danyen aiki.

Rundunar Sojan Amurka ta tabbatar da mutuwar sojojin ta biyu kana wasu sun samu rauni sakamakon hari da aka kai musu lokacin da suke sintirin hadin gwiwa a jiya da sojojin Niger a kudu maso yammacin kasar ta Niger.

Sanarwan tace ko baya ga wadannan sojojin haka kuma an kashe wani sojan dake aiki tare da wannan rundunar sai dai a bayyana ko dan wace kasa bace.

Kawo yanzu ba wata ko wani kungiyar da suka dauki alhakin aikata wannan danyen aikin.

A can kasar Togo kuma, ana ta samun karin kiraye kiraye ga shugaban kasar Togo Faure Gnassingbe da ya sauka daga kan karagar mulki.

Dubban jamaar kasar ne suka yi maci akan babban titin birnin kasar ta Lome a jiya laraba suna kiran shugaban da ya sauka, domin kin bin bukatar tsarin nan na wa’adi zangon mulki sau biyu wanda mahaifin sa ya soke.

Yanzu haka dai Gnassingbe ya shiga zagaye na 3 na mulkin kasar Kenan.

Ko a watan da ya gabata saida aka kashe mutane biyu a lokacin irin wannan zanga-zangar da aka yi jiya, lokacin da jami’an tsaro suka yi anfani da kulki da kuma hayakin nan maisa hawaye ga masu zanga-zangar.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG