Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Wani Babban Masanin Kimiyyar Iran


Inda aka kashe Mohsen Fakhrizadeh a wani gari da ke wajen birnin Tehran a ranar Juma'a, a cewar gidan talbijin din kasar kamar yadda (Fars News Agency ya ruwaito daga AP)

Gidan talabijin din kasar Iran ya ce an kashe wani masanin kimiyyar kasar a wani hari da aka kai – mutumin da Isra’ila ta yi zargin shi ya jagoranci shirin kera makamin nukiliyar sojan Iran har zuwa lokacin da aka wargaza shi a farkon shekarun 2000 a cewar kamfanin dillancin labarai na AP.

Ministan harkokin wajen Iran ya zargi Isra’ila da kisan Mohsen Fakhrizadeh a ranar Juma'a.

Amma Isra'ila ta ki ta ki cewa komai kan kisan, Ko da yake, Firayim Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya taba ambatan sunan Fakhrizadeh a wani taron manema labarai.

Gidan Talabijin din kasar ya ce "wasu gungun 'yan ta'adda ne dauke da makamai" suka kai wa Fakhrizadeh hari.

Ya mutu a karamin asibitin bayan da likitoci da ma’aikatan lafiya suka kasa farfado da shi.

Sakataren Gwamnatin kasar Amurka Michael R. Pompeo

Magoya Bayan Trump Sun Afkawa Ginin Majalisun Amurka

Magoya Bayan Shugaba Donald Trump Sun Mamaye Ginin Majalisar Dokokin Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:56 0:00

Rayuwar Birni

Rayuwar Birni: Hira da Aliyu Danlami mai sayar da furanni a Abuja
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:49 0:00
Karin bayani akan Rayuwar Birni
XS
SM
MD
LG