Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Mummunan Hari a Kabul Ya Yi Sanadiyyar Kisan Mutane 8


Kungiyar 'yan ta'addan IS ta dauki alhakin harin rokokin da aka kai babban birnin Afghanistan.

Jami’ai a Afghanistan sun ce an harba kusan rokoki 24 da suka dira tsakiyar birnin Kabul a safiyar ranar Asabar 21 ga watan Nuwamba, harin da ya yi sanadiyyar kisan akalla mutane 8 tare da jikkata wasu 31. Mai Magana da yawun ma’aikatar cikin gidan kasar Tariq Arian ya ce an harba rokokin ne daga wasu motoci biyu kuma suka sauka kan sassan babban birnin dabam-daban. Ofishin jakadancin Iran da ke Kabul ya ce daya daga cikin rokokin ta kusan fadawa harabar ginin ofishin.

A farkon wannan watan, ‘yan bindigar kungiyar IS uku sanye da damarar nakiyoyi suka afka jami’ar Kabul inda suka kashe akalla mutane 22, galibinsu daliban Afghanistan ne. jakadan Iran a Kabul shi ma ya na cikin ginin ofishin jakadancin a lokacin da aka kai harin, amma ya tsira ba tare da ko kwarzane ba.

Ba tare da bata lokacin ba wani mai magana da yawun mayakan kungiyar Taliban ya fadi cewa kungiyar ba ta da hannu a mummunan harin na yau Asabar.

Kungiyar ‘yan ta’addan IS ta dauki alhakin kai harin, a cewar kungiyar binciken bayanan sirrin SITE da ke bin diddigin ayyukan kungiyoyin ‘yan ta’adda ta yanar gizo.

XS
SM
MD
LG