Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Wani Dan Jamus Da Ake Garkuwa Da Shi A Kano


Wasu 'yan Najeriya suke addu'a a kasuwar dabbobi a Damataru inda aka kai hari

Jami’an tsaro a Najeriya sun ce an kashe wani dan kasar Jamus da ake zargin wata kungiya mai alaka da al-Qaida ta sace cikin watan janairu, lokacin da aka yi kokarin ceto shi.

Jami’an tsaro a Najeriya sun ce an kashe wani dan kasar Jamus da ake zargin wata kungiya mai alaka da al-Qaida ta sace cikin watan janairu, lokacin da aka yi kokarin ceto shi.

Jami’ai suka ce wadan da suke garkuwa da Edgar Fritz Raupach ne suk kashe shi lokacin da jami’an tsaro suka yi kokarin kubatar da shi a wani somame da suka kai a birnin kano.

Wakilin Sashen Hausa a Kano yace rundunar hadin guiwa dake yaki da ta’addanci ce ta kai farmakin, ana sukar lamirin irin wadan nan rundunoni a Najeriya sabo da kasa samun nasarar kubatar da mutsne da ake garkuwa da su da ransu.

Idan za’a iya tunawa cikin watan Maris, wasu da suka yi garkuwa da wani da ingila da Italiya sun kashe su a lokacin da hukumomi suka nemi kai musu doki.

Cikin watan Maris din wata kungiya da ta yi ikirarin tana da alaka da kungiyar al-Qaida dake arewacin Amurka ta gayawa wani kamfanin dillancin labaran Mauritania cewa tana garkuwa da Raupach. Ta nemi a yi musaya da wata mace musulma da aka tsare a Jamus.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG