Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Wani Marubuci A Harabar Wata Kotu A Birnin Amman.


Wata motar daukar maras lafiya, dauke da gawar Naheed Hatter, marubuci da aka kashe a Amman Jordan, rana r lahadin nan.
Wata motar daukar maras lafiya, dauke da gawar Naheed Hatter, marubuci da aka kashe a Amman Jordan, rana r lahadin nan.

An kai mutumin gaban shari'a ne kan zargin batunci ga addinin Islama.

Wani dan bindiga dadi a Jordan, ya harbe ya kashe wani sanannen marubuci dan kasar, a harabar wata kotu, inda aka gurfunar da marubucin, kan zargin cewa, wani zanen barkwanci da ya wallalafa a shafinsa na Facebook, ya muzantawa addinin Islama.

Yau Lahadi, aka harbe aka kashe Nahed Hatter, a gaban ginin wata kotun kasar dake Amman babban birnin kasar.

Kamfanin dillancin labarai na kasar ya bada labarin cewa an kama maharin.
Hatter wanda kirista ne, yace barkwacin ba'a ce ga masu ikirarin jihadi.
Zanen ya nuna wani balarabe da mata biyu, yana cewa, Ubangiji Allah Ya kawo masa giya.

XS
SM
MD
LG