Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Wasu 'Yan China 3 a Janhuriyar Afirka Ta Tsakiya


Shugaban Janhuriyar Afirka Ta Tsakiya Faustin-Archange Touadera da Shugaban China Xi (Shi) Jinping
Shugaban Janhuriyar Afirka Ta Tsakiya Faustin-Archange Touadera da Shugaban China Xi (Shi) Jinping

Da alamar yawan farautar dukiyar Afirka da 'yan China ke yi ba kakkautawa, na cigaba da janyo masu tsana daga wasu 'yan Afrika.

'Yan China akalla uku ne aka kashe, wasu kuma uku su ka ji munanan raunuka, a yankin kudu maso yammacin Janhuriyar Afirka Ta Tsakiya ranar Alhamis, bayan dukan kawo wuka da mutanen wani kauye su masu, saboda zargin cewa su ne su ka sa ruwa ya ci wani sanannen mutumin kauyen.

Wata tawagar 'yan China 10 ne su ka bukaci mutumin mai suna Ignace Dimbele-Nakoe, wanda shugaban matasa ne, da kuma kaninsa, da su masu jagora daga kogin na kauyen Kadei zuwa wurin hakar gwal, bisa ga bayanin mutanen kauyen. Su na tafiya sai karamin jirgin ruwan da su ke ciki ya tintsire har shi Dimbele-Nakoe ya bace cikin ruwa. Daga bisa aka gano gawarsa.

Isar 'yan China ofishin 'yan sandan kauyen don yin bayani ke da wuya, sai mafusatan kauyawan su ka shiga bugunsu da sanduna, gashi kuma 'yan sanda kalilan ne ke wurin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG