Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe 'Yan Ta'adda Goma Sha Daya a Kusa da Kamaru


Sojojin Najeriya Da 'Yan Ta'adda

An kashe ‘yan ta’adda goma sha daya da kame bakwai, a lokacin da Sojojin Najeriya suka budewa wasu gungun 'yan ta’adda wuta dake kokarin tsallakawa kasar Kamaru.

Rahotanni daga Najeriya na nuni da cewa 'yan ta’addan sun fito neman abinci ne daga mafakansu a cikin daji, bayan da suka kasa jure yunwa.

Kakakin Sojojin Najeriya Manjo Janaral Chris Olukolade, yace wannan ne yayi dalilin fadawarsu hannun sojojin dake sintiri akan iyakar Najeriya domin farautar su.

Wadanda aka kama, su suka jagoranci sojojin zuwa mafakar tasu a cikin daji inda akayi gumurzu, kuma aka kara kashe wasu 'yan ta’adda.

An sami makamai kamar bindigogi da boma-bomai, an kuma kwashi babura saba’in, sannan an kuma kashe yan ta’adda hudu a Gombi.

Kakakin rundunar sojoji na ashirin da uku dake Yola, Kaftin Ja'afaru Nuhu yace ana samun nasara a yakin da akeyi da masu tada kayar baya.

Ya kuma bukaci al'ummar dake yankin iyaka dasu taimakawa jami'an tsaro da labarin duk wanda basu amince dashi ba.


please wait

No media source currently available

0:00 0:02:21 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG