Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kawo Karshen Hatsaniya A Tsakanin Amurka Da China


An cinma matsaya da kuma tsagaita wuta a tsakanin kasashen duniya biyu mafi karfin tattalin arziki, Amurka da China.

Amurka da China kasashe biyu mafi karfin tattalin arziki a fadin duniya, sun amince da a tsagaita wuta a fadan da ke tsakanin su na kasuwanci, an cimma wannan yarjejeniyar ne, bayan wata ganawa tsakanin shugabanin biyu Donald Trump da takwaransa Xi Jinging, bayan taron G20.

An samu tattaunawa mai ma’ana da kuma fatar zata kawo cigaba mai dorewa, a tsakanin kasashen biyu Amurka da China, a wani rubuttaccen bayani da shugaba Trump ya fitar, lokacin da yake kan hayarsa ta komawa gida Amurka, daga kasar Argentina a Jirgin Alfarma na Air Force One. Trump ya kara da cewar lallai wannan babbar karramawace gare shi, yayi aiki da shugaba Xi.

Ya kuma shaida wa ‘yan jarida dake cikin jirgin nasa cewar, “Wannan yarjejeniyace mai ma’ana, zan cigaba da rike jadawalin kudin fito, ita kuma China zata cire nata jadawalin" kuma zata dinga siyan kaya da yawa daga Amurka.”

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG