Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kirkiro Munmunan Sabon Nau'in Kwayar Cutar Murar Tsuntsaye


Wasu masana na bincike akan kwayar cutar murar tsuntsaye.

Amurka ta bukaci wasu mujallu biyu da su boye bayanan kirkirar kwayar cutar

Wasu Mujallu guda biyu masu wallafa labaran binciken kimiyya na duba yiwuwar ko su buga bayanan wani bincike akan cutar mura da ake cacar baki a kai bayan da wani kwamitin da ke ba gwamnatin Amurka shawara ya bukace su da, su boye wasu bayanai saboda dalilan tsaro.

Ranar Talata kwamitin da ke ba gwamnatin Amurka shawara akan ayyukan kimiyyar da suka shafi makaman yada cututtuka, ya bukaci Mujallar "Science" ta nan Amurka, da kuma Mujallar "Nature" ta Birtaniya da kar su wallafa bayanai game da kirkiro wata sabuwar munmunar kwayar cutar murar tsuntsaye mai kisa nau'in H5N1.

Cikin sauki sabon nau'in kwayar cutar ke yaduwa tsakankanin berayen masar, wadanda su ma su ke yin mura kamar Bil Adama. A jami'ar Wisconsin da ke garin Madison a nan Amurka da kuma babban asibitin Erasmus na kasar Netherlands, masana ilimin kimiyya su ka kirkiro sabon nau'in kwayar cutar murar tsuntsayen. Kuma gwamnatin kasar Amurka ce ta ba su kudaden gudanar da ayyukan binciken.

Akwai rarrabuwar kanu tsakanin kwararrun masana game da cewa ko ya dace a kirkiro irin wannan munmunan nau'in kwayar cutar murar tsuntsaye. Amma su wadanda suka gudanar da binciken sun ce so suke yi su nazarci yadda kwayar cutar ke rikida, don su gane alamomin da ke nuna cewa wani nau'in kwayar cutar mafi muni ya na bulla. Su kuma masu sukan lamiri sun ce wallafa bayanan dabarar da masanan suka yi amfani da ita wajen kirkiro sabuwar kwayar cutar na iya fadawa hannun 'yan ta'addan da ka iya sake kirkirar kwayar cutar da nufin halaka jama'a.

Amma duk da haka, sauran masana ilimin kimiyya masu gudanar da bincike akan harakokin kiwon lafiya ba su goyi bayan kowace gwamnati ta hana wallafa sakamakon bincike-binciken kimiyya ba.

Mujallun sun amsa bukatar da kwamitin ya gabatar mu su, cikin taka tsan-tsan, su ka ce za su duba yiwuwar boye wasu bayanai, amma sai in gwamnatin Amurka za ta samar da wata hanyar mika cikakkun bayanan da aka rubuta, ga masana ilimin kimiyyar da ke gudanar da ayyukan bincike da gaskiya tsakanin su da Allah.

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG