Accessibility links

Wani tashin hankalin da ya auku a jihar Naija ta arewacin Nijeriya ya yi sanadiyyar kona gidajen Fulani 36 da bacewar dabbobi wajen 70.

An kona gidajen Fulani kimanin 36, banda dabbobi 70 da su ka bace, sanadiyyar wani tashin hankalin da ya biyo bayan tsintar gawar wani mutumin da wasu ke zaton Fulani ne su ka kashe shi a garin Dakogi da ke Karamar Hukuimar Mokwa ta jihar Naijan arewacin Nijeriya.

Wakilinmu a jihar Naija Mustapha Nasiru Batsari ya ce shugabannin Fulanain yankin sun kadu da wannan al’amarin. Mustapha ya ruwaito shugaban kungiyar Miyatti Allah na jihar Naija, Alhaji Samaila Rebe na kiran hukumomin da abin ya shafa da su dau mataki ba tare da bata lokaci ba kuma su yi adalci.


Alhaji Bagga, daya daga cikin wadanda aka kona wa gidaje ya ce hatta na abinci ba su da shi kuma ga yara da tsoffi; sannan kuma a filin Allah su ke. HH Haka su ma Babuga da Majo Bako su ka tabbatar.
A nata bangaren kuma, Gwamnatin Jihar Naija, ta bakin Babban Daraktan Kula Da Ma’aikatar Harkokin Makiyaya Alhaji Mohammed Abubakar Sadik y ace za a gaggauta taimaka ma Fulanin da abin ya rutsa da su.
XS
SM
MD
LG