Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kona Ton 60 Na Jabun Magunguna a Kamaru


Wasu magungunan jabu da aka kama a kasar Ivory Coast. Mayu 3, 2017
Wasu magungunan jabu da aka kama a kasar Ivory Coast. Mayu 3, 2017

Afirka na daya daga cikin nahiyoyin da ake samun magungunan jabu, a baya-bayan nan, wani kame da aka yi a kasar Kamaru ya sa an gano ton 60 na irin wadannan magunguna inda hukumomin kasar suka kona su.

Hukumomi a kasar Kamaru sun kona ton 60 na magungunan jabu da aka kama a kasar a cikin wannan makon.

Wani jami’in kwastam na Kamaru, Marcel Kamgaing, ya ce wadannan magungunan sun hada da na warkar da ciwon sukari, da hawan jini, da sankara ko daji, kuma an shigar da su ne domin sayar wa ga jama’a a kantunan magunguna da kuma gefen hanya.

Ya kara da cewa wadannan magunguna na jabu suna da matukar hatsari ga lafiyar jama’a, kuma suna iya kashe masu amfani da su.

An shirya kona magungunan a daidai lokacin da kasashen duniya ke shirin hallara a kasar ta Kamaru domin yin taro a kan matsalar magungunan jabu a nahiyar Afirka.

Shugaban kungiyar lauyoyi a kasar Kamaru, Jackson kamga, ya ce irin hukuncin da dokokin kasar suka tanada a kan masu sayar da magungunan jabu, baya da tsananin da zai iya zamowa hannunka-mai-sanda ga duk masu shirin shiga wannan mummunan safarar.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG