Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sudan Ta Kudu Ta Janye Jakadunta Daga Kasashe Bakwai


A wani mataki da ba a saba gani ba, kasar Sudan ta Kudu mai fama da rikici ta janye jakadunta daga wasu kasashe bakwai.

Kasar Sudan ta Kudu ta janye jakadunta daga wasu kasashen duniya guda bakwai, amma kasar ta ce wannan matakin ba ya da nasaba da matsalar tattalin arzikin da take fuskanta.

Tabarbarewar tattalin arzikin, wanda ya samo asali daga yakin basasar da aka kwashe shekaru 3 ana yi, ya jefa kasar cikin matsalar karancin kudi, abinda ya sa yawancin jakadun kasar da ke kasashen duniya suka share kamar wattani 6 basu sami albashi ba.

Wata wasika da aka rubata ranar 14 ga watan nan na Yuni, wadda ministan harkokin wajen kasar Deng Alor ya rattabawa hannu, ta ba jakadun Burtaniya, da Sudan, da Uganda da kuma wakilanta a Jamus, da India, da Eretria da kuma Masar wa’adin kwanaki 60 su koma Juba.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar, Makol Ariik, ya tabbatarda gaskiyar cewa gwamnatin Sudan ta Kudu ta janye wasu jakadunta amma ya musanta cewa matakin na da nasaba da matsalolin tattalin arziki.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG