Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kori Wasu 'Yan Sandan Amurka Saboda Mutuwar Wani Bakar Fata


Gwamnatin jihar Minneapolis ta sallami wasu ‘yan sanda hudu da aka samu da hannu a kamen wani ba-Amurka bakar fata da aka yi ranar Litinin wanda ya mutu bayan da wani dan sanda ya danne wuyansa da gwiwa.

Wani da ke tsaye a wurin da lamarin ya faru ya dauki hoton bidiyon, ya kuma sanya shi a kafofin sada zumunci kuma nan da nan ya bazu a fadin kasar.

A shafinsa na Twitter, Magajin garin Minneapolis Jacob Frey ya rubuta cewa sallamar jami’an ‘yan sandan shi ne abin da ya dace.

Sunan mutumin da ya mutu dai George Floyd.

Rundunar ‘yan sandan Minneapolis ta ce Floyd ya yi kama da wani da ake nema ruwa a jallo bisa zargin aikata laifin yin amfani da bayanan wasu.

Ta kuma kara da cewa ‘yan sandan sun yi abin da suka yi ne bayan da Floyd ya ki yarda a kama shi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG