Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An koyawa mata dari sana'o'i a jihar Yobe


Ginin majalisun tarayyar Najeriya
Ginin majalisun tarayyar Najeriya

Dan majalisar wakilai mai wakiltar Potiskum da Nenge dake jihar Yobe Onarebul Sabo Garba shi ya dauki nauyin koyas da mata dari daga sassa daban daban na jihar Yobe sana'o'i domin su fice daga talauci su samu dogaro ga kansu

Onarebul Sabo Garba yace jama'ar dake yankinsa na cikin mawuyacin halin bakin talauci da fatara da kuncin rayuwa.

Mata guda dari da dan majalisar ya dauki nauyin horas dasu kan sana'o'i daban daban an yayesu ne jiya. Yace an zabomata ne da nufin rage radadin talauci dake damun yankin.

Sabo Garba yace lokacin da suke fafutiman neman zabe sun yi alkawura da dama kuma lokaci ya yi yanzu da jama'a da suka zabesu zasu fara gani a kasa dalili ke da ya waiwayi al'ummarsa domin tallafa masu musamman mata da ya bayyanasu a matsayin iyaye da yawancin lokaci wahalu kan koma kansu.

Abubuwan da aka koya masu sun hada da yin sabulu, abun shafawa, man kanshi da kuma turaren gida. Ya kara da cewa an fra da mata ne domin su ne suke daukan nauyin gida da zara wani abu ya faru tare da kula da 'ya'yansu. Yace komenene ya faru mace zata yi kokari ta samar ma 'yalanta abun da zasu ci. Matan da aka fara dasu gwauraye ne da mazajensu sun rasu. Nan da makwanni uku shirin zai horas da mata dari uku.

Dangane da maza Onarebul Sabo Garba yace ya riga ya sayi takardun yin jarabawar share faggen shiga jami'u'i guda dari uku da zai raba wa maza wadanda basu iya cigaba da karatunsu ba saboda wasu dalilai.

Wadanda suka samu horaswar sun bayyana ra'ayoyinsu da yadda suka ji a jikinsu. Sun ce da suna zaune gida basu san abun da zasu yi ba su cigaba da rayuwa amma yanzu sun samu horaswa akan sana'o'i daban daban tare da basu jari da zasu kasuwanci. Sun mika godiyarsu ga Allah da shi dan majalisa Sabo Garba.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:27 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG