Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masana Kimiyya Suna Gwajin Sabbin Hanyoyin Auna Sukari a Jikin Masu Larurin Suga


Google 'contact lense'
Google 'contact lense'

Masana ilmin kimiyya suna gwajin samo wasu hanyoyi masu sauki na auna sukari ta wajen amfani da hawaye.

Mutane da suke fama da cutar sukari suna gwagwarmaya ko wace rana na kiyaye mizanin sukari cikin jininsu, wadda idan ba su takaita yawansa ba, yana iya lahani ga idanunsu, da koda, da kuma zuciya.

Galibi suna auna mizanin sukarin ne ta wajen janyo jini kadan daga jikinsu, amma masana ilmin kimiyya suna kokarin gano wasu hanyoyi masu sauki ta wajen yin gwajin da wasu abubuawa da suke fitowa daga cikin jikin dan adam kamar hawaye.

Kamfanin Google wanda ya shahara a fannin internet ko yanar gizo, yace yana gwaji da tabaron da ake sakawa cikin idanu da ake kira contact da turanci wadanda aka inganta, da zasu iya gargadi ko jan hankalin masu larurin sukari cewa mizanin sukari a jikinsu yayi kasa, mko akasi.
XS
SM
MD
LG