Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Manta Da Wasu 'Yan Najeriya Da Suka Makale A Garin 'Sumy' Da Ke Gabashin Ukraine - Rahotanni


Wasu daliban Najeriya da suka yi nasarar tsallakawa Romania daga Ukraine suna yi wa juna sambarka (AP)
Wasu daliban Najeriya da suka yi nasarar tsallakawa Romania daga Ukraine suna yi wa juna sambarka (AP)

Garin na Sumy da ke arewa maso gabashin Ukraine, na da tazarar kilomita 30 tsakaninsa da Rasha.

Wasu ‘yan uwa da abokan arziki sun yi kira ga hukumomin Najeriya da su kai dauki don kubutar da daliban kasar da dama da suka makale a gabashin Ukraine yayin da Rasha take ci gaba da kai hare-hare.

Mutane da dama sun shiga shafin Twitter suna yekuwar cewa, akwai dalibai da yawa a wani gari da ake kira Sumy da ke gabashin Ukraine inda daliban Najeriya suka kasa fitowa daga yankin saboda yakin da ake yi.

“Kanwata tana @Sumy tare da wasu ‘yan Najeriya. A yau (Alhamis) an kai harin sama kan ginin jami’a, babu kuma hanyar da za su iya ficewa da kansu, suna bukatar taimako.” Oluwatoni Fawole wacce ke amfani da inkiyar @Phloem5 a Twitter ta wallafa a shafinta.

Nan da nan ita ma @IcySpicy26 ta ce, “ni ma kanwata tana wurin.”

“Muna ta fadawa mutane cewa, akwai ‘yan Najeriya da suka makale suna kuma cikin wahala a Ukraine, gwamnati ta ki yin yadda ya kamata.” In ji @josephAdex5.

Ya kara da cewa, “amma masu goyon bayan gwamnatin nan ba sa son jin gaskiya. A ce wai jirgi daya ne tak ya tashi, kwana 8 bayan da aka fara kai hare-hare, Tabdijan!”

Wannan kiraye-kiraye da jama’a ke yi na neman a kai wa ‘yan uwansu dauki na zuwa ne yayin da hukumomin Najeriya suka tura jirage kasashen Poland, Romania, Hungary da Slovakia don kwaso ‘yan kasar da suka tsere zuwa wadannan kasashe da ke makwabtaka da Ukraine.

Shi dai garin na Sumy yana gabashin yankin Ukraine ne da ke makwabtaka da Rasha.

Hasali ma mafi yawan mamayar ta Rasha, ta fi kamari ne a gabashin Ukraine kuma tazarar kilomita 30 ne tsakanin garin da Rashar.

Wani rahoto da gidan talabijin na CNN ya wallafa a shafinsa na yanar gizo a ranar Alhamis, ya ruwaito wata daliba ‘yar Najeriya mai suna Vivian Udenze, tana cewa akwai dalibai baki da yawansu ya haura 600 da suka makale a garin na Sumy.

Ta kara da cewa, daga cikin daliban wadanda mafi aksarinsu suna koyon aikin likitanci ne, akwai ‘yan Najeriya, Tanzania, Morocco, Congo da Tanzania.

A ranar Laraba Najeriya ta fara jigilar kwaso daliban nata a kasahen da ke makwabtaka da Ukraine bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya ware sama da dala miliyan takwas don gudanar da aikin.

XS
SM
MD
LG