Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Matsa Min Na Kaddamar Da Yakin Neman Zaben 2020 - Trump


Shugaban Amurka Donald Trump ya fada a yau Laraba cewa yana cikin matsanacin matsin lamba na ya kaddamar da yakin neman a sake zabensa a zabe mai zuwa da za’ayi a shekarar 2020.

Kamar yadda ya yi a shekarar 2017, yanzun ma ana sa ran cewa shugaban ba zai ba ta lokaci ba wajen ba da sanarwar niyyarsa aa neman a sake zaben nasa.

Sai dai kuma tuni manyan ‘yan siyasan da ake sa ran za su ja da shi suka riga suka kaddamar da nasu yakin neman zaben don janyo hankalin masu jefa kuri’a zuwa ga kyamfen din su.

Kan haka ne a jiya Talata aka fara musayyar bakaken maganganu tsakanin Trump din da mutumen da ake jin za su fafata sosai da shi a zabe mai zuwa, wato Joe Biden, tsohon mataimakin shugaban kasa, wanda ake kyautata zaton zai nemi jam’iyyarsa ta Democrats ta tsaida shi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG