Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Nada Sambo Dasuki A Zaman Sabon Mai Bayarda Shawara Kan Tsaro Na Shugaba Jonathan


Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya

Wannan ya biyo bayan korar ministan tsaro Bello Halliru Mohammed da Janar Patrick Azazi da shugaba Goodluck Jonathan yayi.

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya kori ministan tsaro da kuma mai ba shi shawara kan harkokin tsaron kasa, yayin da ake kara nuna damuwa kan yiwuwar kazancewar tashin hankali a arewacin kasar.

Kakakin shugaban, Reuben Abati, ya bayar da sanarwa jiya jumma’a cewa an cire ministan tsaro Bello Halliru Mohammed, da mai ba shugaba shawara kan harkokin tsaron kasa Janar Patrick Azazi ritaya, daga kan mukamansu.

Yace an nada Kanar Sambo Dasuki mai ritaya, wanda na kusa ne da tsohon shugaba Janar Ibrahim Babangida, a matsayin sabon mai ba shugaba shawara kan harkokin tsaron kasa. Ba a bayyana wanda zai gaji kujerar ministan tsaron kasar ba.

Wannan garambawul a bangaren tsaron Najeriya yana zuwa a yayin da dokar-ta-baci da kuma matakan sojan da ake dauka suka kasa shawo kan fitinar ‘yan Boko Haram wadda ta yi sanadin kashe mutane akalla 90 a cikin mako gudan da ya shige kawai.

Kungiyar Boko Haram ta dauki alhakin wasu hare-haren da aka kai kan Kirista a wasu sassan Najeriya, wadnad su ma suka dauki matakan kai hare-haren ramuwar gayya kan Musulmi.

Wannan fadan ya janyo karin sukar lamirin da ake yi ma gwamnati kan ta kasa shawo kan wannan rikici bisa damuwar cewa idan har gwamnatin ba zata iya dakile hare-haren da ‘yan Boko haram ke kaiwa ba, ana iya samun karin jama’ar da zasu dauki matakan kansu na ramuwar gayya ko kai hare-hare.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG