Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Nemi Lallai a Tsagaita Wuta a Libiya a Tattaunawar Birnin London


Babban Taron manyan kasashen duniya akan makomar siyasar kasar Libiya.

Ma'aikatan diflomasiyyar manyan kasashen duniya da ke tattaunawa a birnin London sun bukaci da lallai a tsagaita wuta a kasar Libiya.

Jami'an diflomasiyyar manyan kasashen duniya da ke taro a London, babban birnin kasar Birtaniya, sun bukaci da lallai a tsagaita wuta a kasar Libiya.

Babban Magatakardan Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon ya fada a yau talata cewa manyan kasashen duniya na shirya wani irin gagarumin kokarin taimakawa a daidai lokacin da su ke tsarawa kasar Libiya makomar siyasa bayan Moammar Ghadafi.

Frayim Ministan kasar Birtaniya, David Cameron ya yi kukan cewa sojojin da ke biyayya ga shugaba Moammar Ghadafi na kai hare-haren kisan jama'a a birnin Misrata a daidai lokacin da masu adawa ke ci gaba da fafatawa da sojojin masu goyon bayan gwamnatin kasar Libiya.

Da ya ke bude zaman tattaunawar akan makomar kasar Libiya, Cameron ya ce Ghadafi na ci gaba da keta haddin kudirin Majalisar Dinkin Duniyar da ya bayar da izinin yinamfani da karfi a kare lafiyar fararen hula.

Sakatariyar harakokin wajen Amurka Hillary Clinton ta ce manyan kasashen duniya sun hana yin kisan kasko ga jama'a, ta hanyar kai hare-haren jiragen saman yakin da su ka kassara sojojin Mr.Ghadafi. Ta kara da cewa za a ci gaba da yin ruwan wuta har ya zuwa lokacin da Mr.Ghadafi zai saurari Majalisar Dinkin Duniya.

Duk da babban taron na London, ana ci gaba daluguden wuta a kasar Libiya.
Duk da babban taron na London, ana ci gaba daluguden wuta a kasar Libiya.

Ministocin harakokin wajen kasashe kimanin Arba'in ne ke halartar babban taron na yau talata, wanda ake yi da nufin samar da wani shirin kawar da Mr.Ghadafi daga mulki.

XS
SM
MD
LG