Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Rantsar Da Sabon Shugaban Kasar Malawi


Lazarus Chakwera

An rantsar da sabon shugaban kasar Malawi Lazarus Chakwera domin wa’adin mulki na tsawon shekaru 5 a yau Lahadi, ‘yan sa’o’i bayan cire tsohon shugaban kasar Peter Mutharika a zaben da aka sake gudanarwa.

Chakwera mai shekaru 65, ya lashe kashi 58.5 cikin dari na yawan kuri’un da aka kada a ranar Talata, wanda ya sauya sakamakon zaben na farko a watan Mayun shekara ta 2019, wanda kuma kotuna suka soke.

Masu fashin baki na bayyana sake zaben da aka yi a zaman wani zakaran gwajin dafin karfin da kotuna su ke da shi a Afirka, na magance magudin zabe, da kuma hana shugaban kasa amfani da karfinsa a zaben.

“Tare da taimakon ku, za mu dawo da fata a zukatan al’umma masu tasowa, na samun gwamnati da za ta yi wa jama’a aiki, ba wai ta mulke su ba”, Chakwera ya fada a jawabin da ya yi wa dimbin jama’ar da suka tattaru a bikin rantsarwar.

Jam’iyyar MCP ce ta farkon kafuwa a kasar ta Malawi, kuma nasarar Chakwera ta sake maido da ita kan mulki bayan shekaru 26 na mulkin adawa.

Bangaren shara’a na kasar ya rusa sakamakon zaben da aka gudanar a watan Mayun shekara ta 2019 da ya baiwa tsohon shugaba Mutharika wa’adin mulki na 2 bisa dalilan tafka magudin zabe, kana ta ba da umarnin sake gudanar da zaben.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG