Accessibility links

An Rantsar da Joyce Banda, Mace Ta Farko, Shugabar Kasar Malawi.

  • Aliyu Imam

Shugabar kasar Malawi, mace ta farkoJoyce Banda, take jawabi ga manema labarai Asabar.

Asabar din nan akayi bikin rantsar da mataimakiyar shugaban kasar Malawi, Joyce Banda, shugabar kasa, anyi bikin ne a babban binrin kasar Lilongwe.

Asabar din nan akayi bikin rantsar da mataimakiyar shugaban kasar Malawi, Joyce Banda, shugabar kasar, anyi bikin ne a babban binrin kasar Lilongwe.Hakan ya biyo bayan tabbar da mutuwar shugaba Bingu wa Mutharika, wanda kwatsam bugun zuciya ta kashe shi ranar Alhamis.

Madam Banda, wacce itace mace ta farko da ta zama shugabar kasar Malawi, anyi mata korar kare daga jam’iyyar mai mulkin kasar, a 2010. Amma taci gaba da rike mukaminta na mataimakiyar shugaban kasa, har kashi yanzu kuma ta dare kujerar shugabncin kasar kamar yadda tsarin mulki ya tanadar. A jawabinta na kama aiki, tayi kira da a hada kai, ta mai cewa “babu lokaci na ramuwar gayya”.

Tace tayi kyakkyawar tattaunawa da wakilan majalisar ministocin kasar tunda farko a wunin Asabar, ta kira ganawar matakin farko na magance matsaloli da suke addabar kasar. Ta kuma godewa illahirin ‘yan kasar wadanda suka mutunta tsarin mika mata mulki da aka yi cikin lumana.

Kodashike shugaba Mutharika ya raasu tun ranar Alhamis sakamakon bugun zuciya, gwamnati ta jinkirta tabbatar da labarin har zuwa Asabar din nan, yayinda ake ta yada jita jita kan halin da marigayin shugaban yake ciki. Jinkirin da aka yi wajen tabbatar da labarin, yasa aka fara bayyana damuwar cewa magoya bayan shugaban kaa mai rasuwa suna kitsa hanyoyinda zasu bi su aza dan jam’iyyar mai mulki a matsayin shugaban kasa.

XS
SM
MD
LG