Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Rantsarda Sababbin Shugabannin Yankunan Kananan Hukumomin Jihar Yobe a Nigeria


Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Ibrahim Geidam
Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Ibrahim Geidam

Bayanda aka rantsar da su, sababbin shugabannin yankunan kananan hukumomin jihar Yobe sunyi alkawarin wa jama’a aiki, Gwamna Geidam kuma na zargin ‘yan adawa da yi wa jihar zagon kasa.

Karshenta dai anyi gagarumin shagalin rantsarda shugabannin yankunan kananan hukumomi 17 na jihar Yobe da aka yi zabensu a ranar Assabar da ta wuce. Gwamnan jihar Yobe, Ibrahim Giedam, wanda ya yi jagorancin shagalin da aka yi a Damaturu, fadar gwamnatin jihar Yoben, ya caccaki ‘yan adawar da suka yi zargin cewa an kashe mutane da dama a lokacin zaben, abinda gwamnan yace karya ne. Su ma sababbin shugabannin yankunan kananan hukumomi sun yi alkawarin cewa zasuyi aiki tukuru wajen biyan bukatocin al’ummar yankunansu. Wakilin Muryar Amurka, Haruna Dauda, ya halarci bikin rantsuwar kuma ya aiko mana wannan rfahoto:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG