Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Rattaba Hannun Yarjejeniyar Zama Lafiya A Sudan


Sudan Peace Deal
Sudan Peace Deal

A jiya Litinin gwamnatin rikon kwarya ta Sudan ta rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da dakarun juyin juya hali na Sudan (SRF), wata gamayyar kungiyoyin yan tawaye daga yankunan Darfur, Kudancin Kordofan da kuma Blue Nile.

Yarjejeniyar mai cike da tarihi, da aka kulla bayan shafe shekara ana tattaunawa da Sudan a Kudu, ta yi tanadin raba mukamai, hade jami’an tsaro, ‘yancin kasa, da kuma dawo da wadanda suka bar muhallansu a cikin shekarun da aka kwashe ana rikici.

sudan agreement
sudan agreement

Bangarori biyu na ‘yan tawaye da suke cikin kungiyar ‘yan tawaye ta SLM da SPLM-N sun ki shiga cikin yarjejeniyar ta zaman lafiyar. Amma mai magana da yawun gwamnatin rikon kwaryar Sudan, Faisal Salihi ya yaba da yarjejeniyar.

Ya ce zaman lafiya shi ne akan gaba daga cikin abubuwa 10 da gwamnatin rikon kwarya ta kudiri aniyar magance su. Ya ce tun a watan Satumban bara wakilai suka hadu a Juba kana suka sanar da Ayyana yarjejeniyar Juba. Salih ya ce gwamnatin rikon kwaryar tana farin ciki na cimma wannan mataki amma suna sane da cewa har yanzu akwai zagayen tattaunawa da ake bukata tare da kungiyoyin ‘yan tawaye na SLM da SPLM-N. Domin fatan cimma cikakkiyar yarjejeniyar zaman lafiya da kowa zai amince da ita.

‘Yan tawayen sun gwabza fada tare da dakarun da tsohon shugaban kasa Omar al-Bashir ya tura, wanda sojoji suka hambarar da shi a watan Afrilun 2019 bayan shafe watannin ana zanga zanga kana aka maye gurbinsa tare da gwamnatin hadaka tsakanin sojoji da farar hula.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG