Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sa Ma Wani Titin Birnin Washington Sunan Kungiyar Kare Bakake


Magajiyar Birnin Washington D.C.
Magajiyar Birnin Washington D.C.

Jiya Jimma’a Magajiyar Garin Birnin Washington, D.C., Muriel Bowser, ta sa ma wani titi mai zuwa Fadar White House suna “Black Lives Matter Plaza,” wato shirayin kungiyar fafatukar kare ‘yancin bakake ta “Black Lives Matter,” saboda jinjina ma masu zanga zangar da ke fafatukar ganin an yi sauye sauye, biyo bayan mutuwar George Floyd, wani ba Amurke bakar fata, a hannun ‘yan sanda a Minneapolis.

Wani mai zane-zane tare da wasu jami’an hukumar birnin sun fara aikin rubuta kalmar “Black Lives Matter” baro-baro da asuba a kan titin da ke kaiwa dandalin Lafayette Park wanda ke ketaren fadar White.

With the Washington Monument in the background people walk on the street leading to the White House after the words Black Lives Matter were painted on it by city workers and activists Friday, June 5, 2020, in Washington. (AP Photo/Manuel Balce Ceneta)
With the Washington Monument in the background people walk on the street leading to the White House after the words Black Lives Matter were painted on it by city workers and activists Friday, June 5, 2020, in Washington. (AP Photo/Manuel Balce Ceneta)

(Sunan 'Black Lives Matter' baro-baro kan titin birnin Washington)

A wata takaitacciyar hidima, ma’aikatan hukumomin birnin sun kafa wasu alamomin da ke nuna sabon sunan hanyar kuma, Bowser, yayin da ta ke jawabi ga taron jama’a, ta ce, “A Amurka, kowa na iya gangami cikin lumana.”

Sake sunan hanyar na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan da magajiyar garin ta shafe kwanaki ta na adawa da kasancewar jami’an tsaron da gwamnatin tarayya ta tura da kuma irin matakan da sojoji su ka dauka kan zanga zangar da aka shafe kwanaki ana yi babban birnin kasar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG