WASHINGTON, DC —
Yanzu haka a jihohin Adamawa da Taraba, kamar sauran jihohi an fara tattara alkalumman sakamakon zabe daga kananan hukumomi, yayin da tuni har yan takarar gwamna suka fara maida martani game da sakamakon da aka fara samu.
A jihar Taraba, baya ga harin da wasu yan bangan siyasa suka kai a Takum, haka nan kuma kamar yadda rahotanni ke nunawa a kyau yankunan da aka sace akwatunan zabe ciki kuwa har da karamar hukumar Wukari dake kudancin jihar.
Ga rahotan daga Ibrahim Abdul’Aziz.