Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sace Amurkawa Biyu A Hanyar Kafanchan Zuwa Abuja


Masu satar mutane da 'yan fashi sanye da kayan soja, a bayan da 'yan sandan Najeriya suka kama su

An kuma kashe 'yan sanda biyu dake rakiya ma wadannan Amurkawa biyu da 'yan kasar Canada su biyu wadanda su ma aka sace su a wani wurin dake cikin karamar hukumar Kagarko a kan wannan hanya

'Yan bindiga sun sace Amurkawa biyu da wasu 'yan kasar Canada su biyu a cikin Jihar Kaduna dake yankin tsakiyar Najeriya.

Wani kakakin rundunar 'yan sanda ya fadawa VOA cewa an kuma kashe jami'an 'yan sanda biyu da suke rakiya ma wadannan turawa dake kan hanyar komawa Abuja daga garin Kafanchan.

Kakakin 'yan sandan na Jihar Kaduna, Mukhtar Aliyu, yace "'yan sanda biyu dake reakiya ma turawan, sun yi musanyar wuta da masu sace mutanen na tsawon lokaci, abinda ya kai har suka rasa rayukansu."

Wakilin Muryar Amurka, Nasiru Yakubu, yace 'yan bindigar sun tare hanya suka sace mutanen ne a tsakanin Jere da Kargo, a kan wannan hanya da a yanzu ta yi kaurin suna wajen fashi da satar mutane.

A shekarar da ta shige ma, an sace wani bature dan kasar Jamus a wannan hanya.

Haka kuma a daidai wannan wurin ne a 'yan watannin baya aka sace tsohon ministan wasanni na Najeriya, Damishi Sango, wanda shi ma yake kan hanyarsa ta zuwa Abuja.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG