Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sace ‘Yan kasuwar Kantin Kwari 20 a Hanyarsu Ta Zuwa Kudancin Najeriya


Gwamnan Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje

Rahotanni daga jihar Kogin Najeriya na cewa, masu garkuwa da mutane da suka sace wasu ‘yan kasuwar Kantin Kwari da ke Kano, sun nemi a biya su kudaden fansa.

Hadaddiyar kungiyar ‘yan kasuwa ta Arewacin Najeriya ta tabbatar da sace wasu mambobinta sama da 20 da ke kan hanyarsu ta zuwa kudancin Najeriya.

Wasu rahotannin sun ce ‘yan kasuwar sun haura 20 yayin da wasu ke cewa ba su kai haka ba.

‘Yan kasuwar, wadanda suka fito daga kasuwar Kantin Kwari da ke Kano, na hanyarsu ne ta zuwa siyo hajoji a babban birnin kasuwancin nan na Aba, da ke jihar Abia a kudu maso gabashin Najeriya.

Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis a tsakanin jihohin Kogi da Edo kuma kawo yanzu ‘yan bindigar da suka sace ‘yan kasuwar sun mika bukatar a biya su kudaden fansa kafin su sake su.

“Da tun ana miliyan 30-30 sai aka ce 20-20, to yanzu kuma abin ya juya, ana maganar za su fadi kudin da za a bayar gaba daya a karbe su, wato za a ba da miliyan 20, to a ina za a samu miliyan 20? Malam Abubakar, daya daga cikin ‘yan uwan wadanda aka sace ya fadawa Muryar Amurka.

Ya kara da cewa, bayanan da suka samu, sun nuna cewa, wadanda suka kwashe ‘yan kasuwar na sanye ne da kayan soja.

Malam Bashir Uba Hassan, sakatare a kungiyar ‘yan kasuwar arewacin Najeriya, ya tabbatar da aukuwar wannan lamari.

“Motar da aka sace su, ta kan dauki mutum 54, kuma wani lokacin mu kan dauki hayar motar baki dayanta.” Hassan ya ce.

Farfesa Bello Bada, na jami’ar Usman Dan Fodio a jihar Sokoto, wanda kan yi sharhi kan al’amuran yau da kullum ya ce “wannan al’amari (na satar mutane) yana neman ya buwayi duk wani abu da ake zato.”

Matsalar satar mutane domin neman kudin fansa dai ta zama babban kalubale a Najeriya musamman ma a arewaci, lamarin da kan kai ga asarar dumbin dukiyoyi wani lokaci ma har da rayuka.

XS
SM
MD
LG