Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Saka Dokar Hana Fita A Jihar Rivers


Wani yankin Yola da aka saka dokar hana fita a Najeriya
Wani yankin Yola da aka saka dokar hana fita a Najeriya

A Jihar Rivers da ke kudu maso kudancin Najeriya, an saka dokar hana fita bayan zanga zangar da ta biyo bayan bayyana sakamakon zaben kuri'un da 'yan jihar suka kada a zaben shugaban kasa.

Hukumomi a Jihar Rivers sun saka dokar hana fita bayan da aka yi wata zanga zanga yayin da aka bayyana sakamakon zaben jihar.

A daren jiya gwamnatin jihar ta ba da umurnin kowa ya zauna a gida bayan barkewra rikici.

Kakakin Rundunar ‘yan sandan jihar Ahmad Muhammad ya ce gwamnatin ta yi hakan ne saboda ta kare rayuka da dukiyoyi.

“Ita gwamnatin jiha ta duba ta ga ya cancanta a saka wannan doka saboda a kare duk wani abu da zai biyo baya na tashin hankali.” In ji Muhammad.

Game da batun lokacin da za a dage dokar, kakakin y ace za a duba a tabbatar cewa al’amura sun daidata kafin a dage dokar.

“Ita dai gwamnatin jiha ta ce za ta duba taga har sai al’amura sun daidaita sannan ta fara sassautawa har zuwa lokacin da ta ga ya dace a janye dokar.” Ya kara da cewa.

Rundunar ‘yan sadan ta kuma musanta zargin da ke cewa an harba yaji mai saka kwalla akan masu zanga zangar.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG