Accessibility links

An sake arangama a arewacin Nijeriya har wadanda su ka mutu sun kusa kaiwa 100 a yanzu

  • Ibrahim Garba

Wasu daga cikin wuraren da aka kai hare-hare

Arangama ta sake barkewa tsakanin matasan Kirista da Musulmi a arewacin Nijeriya a jiya Laraba, wanda ya sa adadin wadanda su ka halaka a tashin hankalin na kwanaki hudu ya kusa kaiwa 100.

Arangama ta sake barkewa tsakanin matasan Kirista da Musulmi a arewacin Nijeriya a jiya Laraba, wanda ya sa adadin wadanda su ka halaka a tashin hankalin na kwanaki hudu ya kusa kaiwa 100.

An yi ta arangamar ce duk ko da dokar hana fita sam-sam a biranen Kaduna da Damaturu. Shaidu sun ba da rahotannin kasancewar dinbin sojoji masu sintiri bisa tituna.

Jerin tashe-tashen hankulan sun samo asali ne daga ranar Lahadi, bayan da tsattsaurar kungiyar Islamar nan ta Boko Haram ta kai hari kan Majami’un Kirista 3 a jihar Kaduna. Hare-haren kunar bakin waken sun haddasa mutuwar mutane 21, wanda ya sa Kirista su ka kai hare-haren daukar fansa kan Musulmin da ya haddasa mutuwar karin mutane 52.

A ranar Litini, wasu da ake zargin ‘yan Boko Haram ne sun kai hari kan ‘yan sanda da wasu jami’an tsaro a garin Damaturu. An cigaba da musayar wuta tsakanin jami’an tsaro da ‘yan bindigar har zuwa ranar Talata, wanda ya haddasa mutuwar mutane 40.

Hukumomi dai na zargin Kirista da Musulmi da laifin tayar da fitinar.

Kungiyar Boko Haram dai ta ce ta na yaki ne don kafa kasar Musulunci, kuma ba ta yadda da halalcin gwamnatin Nijeriya da kuma kundin tsarin mulkin kasar ba.

Ra’ayinka

Show comments

XS
SM
MD
LG