Accessibility links

An Sake Dakatar Da Jiragen Kamfanin Dana

  • Ibrahim Garba

Baraguzan jirgin Dana da ya yi hatsari bara

Hukumar Kula Da Zirga Zirgar Jiragen Sama ta Nijeriya ta dakatar da jiragen kamfanin DANA don gudanar da wani bincike.


A karo na uku an dakatar da zirga-zirgar jiragen saman na kamfanin DANA. Wannan matakin da Hukumar Kula Da Zirga-zirgar Jiragen Sama ta kasa ta dauka ya biyo bayan dakatar da zirga-zirgar jiragen saman kamfanin Associated Air wanda wani jirginsa ya yi hatsari a satin da ya gabata.


Wakilinmu na Lagos, Ladan Ibrahim Ayawa ya ruwaito mai magana da yawun hukumar, Yakubu Datti na cewa an dakatar da kamfanin DANA din ne don a yi wani dan bincike don a san abin yi nan gaba. Ya ce duk hakan na cikin hurumin aikinsu. Y ace kamar yadda dan sanda ke da hurumin tsai da mota a kowane lokaci ya yi bincike, haka ma hukumar su ke da ikon dakatar da zirga-zirgar duk wani kamfanin jirgin sama don gudanar da bincike. Y ace muddun aka tarar cewa kamfanin bai da wata matsala to zai cigaba da zirga-zirgar jiragensa. Kuma game da zargin cewa ba su daukar mataki sai ta baki kuwa Datti ya yi nuni da yadda su ka dakatar da tashin jiragen wasu gwamnoni sai aka alakanta abin da siyasa.
To saidai kuma da Ladan ya tuntubi Mataimakin Sakataren Kungiyar Masu Kamfanonin Jiragen Sama, Muhammad Tukur, y ace wannan al’amarin dai ya zama rudu saboda kamfanin DANA da kansa ya tsayar da tafiyar wani jirginsa don kare lafiyar fasinjoji sai kuma gashi an dakatar da cigaba da tashin jirginsa. To saidai daya daga cikin daraktocin kamfanin jirgin saman mai suna Francis Ogboro y ace sun a sane da abin da ake ciki kuma suna shirye don duk wani bincike.

XS
SM
MD
LG