Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sake Kashe a Kalla Mutane 6 a Birnin Mogadishu


Jini ne shafe jikin wata hanyar cikin otal din Muna a birnin Mogadishu, 24 ga Agusta.

An Sake Kashe a Kalla Muatane 6 a Cigaba da Yamutsi a Birnin Mogadishu.

Yaki ya kara tsananta a babban birnin kasar Somaliya, kwana guda bayan da masu tsattsauran ra’ayin Musulunci su ka kai hari kan wani otal su ka kashe fiye da mutane 30.

Shaidun gani da ido sun ce mayakan sakan kungiyar al-Shabab da sojojin gwamnati sun yi ta musayar wutar bindigogin atilare yau Laraba. An bada rahoton kashe a kalla mutane 6.

Kwamandojin dakarun gwamnati sun ce sun ja daga a tungayensu sanadiyyar harin da al-Shabab ta kai da dare.

Jiya Talata ne dai dakarun al-Shabab su ka kai hari kan wani otal da ke a daya daga cikin ‘yan wuraren da ke karkashin ikon gwamnati. A wata sanarwar da ta fito da ita yau Laraba, Ma’aikatar Yada Labaran Somaliya ta ce mutanen da suka mutu sanadiyyar harin sun kai 33, ciki har da wasu ‘yan Majalisar Dokokin kasar.

XS
SM
MD
LG