Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ambaliya a Junhuriyar Nijer


A Nigerois boy looking at the Niger River near Zinder. Aid agencies warn of a 'double disaster' for millions of people in Niger where heavy rains and flooding are compounding food shortages caused by a prolonged drought.

Ambaliyar ruwa ta sake cakuda al’amurra a Junhuriyar Nijer inda al’umma ke fama da yunwa.

Kungiyoyin bada agaji na kasa-da-kasa sun ce ambaliyar ruwan da ta abkawa Junhuriyar Nijer ta nakkasa kayan anfanin gona mai yawa, ta kuma tayar da mutane sunfi dubu 100 daga gidajensu, sannan kuma ta kara cakuda matsanancin halin rashin isasshen abincin da daman kasar ke fuskanta. Ko a birnin Yamai, ance yanzu Kogin Niger ya kure iyakarsa, wanda aka ce shine karo na farko da aka ga hakan a cikin shekaru 80. Cibiyar bada agaji ta Ingila ta Oxfam tace wannan ambaliyar tayi awon gaba da gidajen jama’a da dama, da lambunansu da kuma faddamunsu na shinkafa. Oxfam kuma tace ambaliyar ta ma toshe hanyoyi da dama da za’a so bi ta kansu, a kai agaji ga wa’anda abin ya shafa. Ta kuma fadi cewa izuwa yanzu an tabattarda cewa akalla mutane shidda ambaliyar ta aika su Barzahu. Daman tun ma kafin zuwan wannan ambaliyar, mutane kamar milyan 8 ke fama da masifar yunwa a Junhuriyar at Nijer, kuma MDD ta fada cewa, muddin ba karin taimako aka samu ba, ba’a san yadda za’a ciyarda kamar kashi 40% na mutanen NIjer dake fama da karancin abincin ba.

People standing near homes destroyed by flooding near Zinder.
People standing near homes destroyed by flooding near Zinder.

XS
SM
MD
LG