WASHINGTON, D.C —
Hukumar Lafiya Ta Duniya WHO ta tabbatar da sake barkewar cutar nan ta Ebola a Jamhuriyar Demokaradiyyar Congo (DRC), a daidai lokacin da barkewa ta fako ta fara nuna alamar kawowa karshe.
A wani taron manema labarai da ya yi a birnin Geneva a jiya Litini, Shugaban Hukumar ta WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce wannan sabuwar barkewar ta auku ne daura da birnin Mbandaka da ke Lardin Equateur na arewa maso yammacin kasar.
Gwamnan lardin ma, Bobo Boloko Bolumbu, ya tabbatar da mutuwar mutum hudu sanadiyyar cutar.
A 2018, lardin na Equateur ya yi fama da barkewar cutar ta Ebola, wadda ta kashe mutum 33 kafin a shawo kanta.
Za ku iya son wannan ma
-
Maris 07, 2021
Za Mu Kotu Don Kalubalantar Sakamakon Zabe - Mahamane Ousman
-
Maris 04, 2021
Kotun Kolin Ghana Ta Tabbatar Da Sake Zaben Akufo-Addo
Facebook Forum