Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sake Sassauta Dokar Hana Fita a Kaduna


Wasu 'yan sandan Najeriya a wani shingen bincike a jihar Kaduna
Wasu 'yan sandan Najeriya a wani shingen bincike a jihar Kaduna

Sanarwar ta kara da cewa, hukumomin jihar sun dauki wannan matakin ne, bayan wani zama da aka yi a yau (Laraba) domin yin dubi kan yanayin tsaro a jihar.

Hukumomin jihar Kaduna da ke arewa maso yamamcin Najeriya, sun kara rage sa’o’in dokar hana zirga zirga da aka saka bayan rikicin da ya barke a jihar a karshen makon da ya gabata.

“Daga gobe 25th ga watan Oktoba 2018, al’umar jihar Kaduna za su iya fita wuraren sana’o’insu daga 6 na safe zuwa 5 na yamma.” Inji wata sanarwa dauke da sa hannnun mai bai wa gwamnan jihar shawara kan harkar yada labarai, Samuel Aruwan.

Sanarwar wacce Muryar Amurka ta samu, ta kara da cewa, hukumomin jihar sun dauki wannan matakin ne, bayan wani zama da aka yi a yau (Laraba) domin yin dubi kan yanayin tsaro a jihar.

Ana sa ran harkokin kasuwanci kamar na banki da sauran wuraren hada –hada da makarantu su bude a goben.

Jihar ta Kaduna ta fuskanci tashin hankali mai nasaba da addini da kabilanci inda aka samu asarar rayuka da dumbin dukiyoyi, lamarin da ya sa gwamnatin ta saka dokar hana fita na tsawon sa'o'i 24.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG