Accessibility links

An Sake Yiwa Wata Mace Fyaden Taron Dangi A Indiya

  • Grace Alheri Abdu

Mata sun taru domin yiwa budurwar da aka yiwa fyaden taron dangi addu'a
‘Yan sandan kasar Indiya sun ce sun kama wadansu mutane shida da ake zargi da yiwa wata mace fyade, bayanda suka sace ta a cikin motar safa, makonni bayan da irin wannan fyaden taron dangin da aka yiwa wata daliba ya girgiza kasar.

Hukumomi sun ce wadda aka yiwa fyaden ‘yar shekaru 29 ita kadai ce fasinja a motar safar yayinda take tafiya zuwa kauyensu dake jihar Punjab dake arewacin kasar ranar jumma’a.

Bisa ga cewar wadda aka yiwa fyaden, direban motar ya shiga wani lungu inda shi da Karen motar da abokansu biyar suka yi mata taron dangin kafin suka sauke ta a kauyensu ranar asabar da asuba.

Yan sanda sun kama mutane shida dangane da lamarin bayanda da macen ta kai kara ranar asabar. Wani kakakin ‘yan sanda yace mutanen sun amsa aikata laifin.

A halin da ake ciki kuma, mutane shida da ake zargi da yiwa wata mace ‘yar shekaru 23 kazamin fyaden taron dangi bayanda suka dauke ta da wani abokinta a motar safa a New Delhi watan da ya gabata zasu gurfana gaban kotu a wata shari’a da za a gaggauta. Za a yi shari’ar mutum na shida wanda shekarunsa basu kai sha takwas ba a wata kotu ta kangararrun yara.
XS
SM
MD
LG