Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sake Zaben Shugaban Turkiyya Racep Tayyip Erdogan


An sake zaben shugaban Turkiyya Racep Tayyip Erdogan a matsayin shugaban kasa, inda ya sami fiye da rabin kuri’un da aka kada.

Da farko jam’iyyar adawa ba ta amince da sakamakon zaben ba, amma daga baya madugun adawar ya amince. Erdogan ya kara hawa kan kujerar mulki yanzu don wani wa’adin.

Masu goyon bayan shugaba Erdogan, sun yi ta murna a fadin kasar a lokacin da suka sami labarin nasarar da ya samu. A cewar kamfanin dillancin labaran Turkiyya, Erdogan ya sami kuri’u kusan kashi 53 cikin dari. Shugaban dan shekaru 64 da haihuwa, yayi jawabin samun nasara a helkwatar jam’iyyarsa dake birnin Ankara.

Erdogan ya ce ya sami sakon da ‘yan kasar suka tura mashi ta kuri’unsu, ya kara da cewa yanzu zai kara kaimi wajen aiki da karin goyon bayan da ya samu a zaben.

Da farko jam’iyyar adawa ta ki ta amince da sakamakon zaben, tana mai ikirarin cewa, an sanar da sakamakon bayan ba a gama kirga kuri’u ba. Wasu hotuna da suka bayyana a shafukan sada zumuncin sun nuna buhunan kuri’u da ake zargi ba a kirga ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG