Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Saki Shugaban Burkina Faso Michel Kafando


Janar Gilbert Diendere a Ouagadougou.

Shugabannin juyin mulkin ne suka bayyana haka cikin wata sanarwa da suka bayar.

A Burkina Faso shugabannin da suka ayyana juyin mulki sun bada labarin sun saki shugaban wucin gadi na kasar Michel Kafando a zaman wani mataki na nuna kyakkywar niyya a bnagarenta, bayan da suka kifar da gwamnatin kasar ranar Laraba.

A ciki wata sanarwa da jagororin da suka yi juyin mulkin suka bayar sun ce Mr. Kafando yana gidansa na gwamnati, suka kara da cewa matakin sakin nasa, alamace ta cewa "zaman dar-dar da kasar ta shiga ya fara sauki". Shugaba Kafando wanda suka tsare lokacinda dogarawan tsaron shugaban kasar suka kutsa cikin wani taron majalisar ministocin kasar ranar laraba bai fito a bainar jama'a ko ya fidda wata sanarwa ba tun lokacin.

PM kasar Isacc Zida wanda aka tsare shi lokaci daya da shugaban kasar, har yanzu ana ci gaba da yi masa daurin talala.

Jiya Jumma'a kunigyar hada kan kasashen Afirka AU ta dakatar da Burkina Faso da dukkan maua'amala da kungiyar saboda juyin mulkin, ta kuma yi barazanar azawa shugabannin juyin mulkin takunkumi ida basu saki shugaban na wucin gadi da kuma PM ba.

Majalisar tsaro ta kunngiyar ta bada sanarwar hakan bayan wani taro da tayi a Addis Ababa, helkwatar kasar Habasha. Majalisar ta fada a shafinta na Twitter cewa, ba zata amince ko ta goyi bayan duk wani shirin mika mulki ga farar hula sabanin wanda kasar ta ayyana cikin watan Nuwamban bara.

Haka nan a jiya jumma'a, shugabannin kasashen Senegal da Benin, sun je Burkina domin fara shawarwari da madugun juyin mulkin Janar Gilbert Diendere.

XS
SM
MD
LG