Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Saki Tsohon Shugaban 'Yan Tawayen DR Congo


Tsohon Shugaban Yan Tawayen DR Congo, Jean-Pierre Bemba

Kotun manyan laifuka ta kasa da kasa ta bada umarni a saki tsohon shugaban yan tawayen kasar Demokaradiyar Jamhuriya Congo, wanda yanzu shine mataimakin shugaban kasar Jean-Pierre Bemba.

Kotu ta wanke Bemba ne a ranar Juma'a daga zargin aikata laifukan yaki da na cin zarafin bil adama.

Sai dai an ci gaba da rike shi har sai kotu ta yanke hukunci a kan wani zargi na dabam na bada cin hanci ga mai masa sheda.

Alkalai masu shari'a sun bada umarni jiya Talata a saki Bemba daga kurkuku, yayin da zai jira har sai an yanke hukunci a kan wannan batu.

Kungiyar rajin kare hakkin bil adama ta Amnesty International, ta kwatanta sakin Bemba da babbar kalubala ga wadanda yaci zarafinsu a cikin ayyukansa na fiyade da cin zarafi ta jima'i.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG