Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sako Dan Birtaniya Na Karshe Daga Guantanamo


Wasu Masu Fafutukar Kare Hakkin Bil Adama Rike Da Hoton Shaker Aamer.

An sako dan kasar Ingila na karshe dake tsare a gidan kurkukun nan na Amurka dake kan tsibirin Guantanamo a kasar Cuba.

A yau Juma’a sakataren harakokin wajen Biritaniya, Philip Hammond ya tabattar da cewa an sako Shaker Aamer, wanda asalinsa dan kasar Sa’udiyya ne.

Kuma a yau din ake sa ran Aamer zai isa Ingila.

Tun shekarar 2002 aka tsare shi a wannan gidan kason ba tare da an tuhumce shi da wani laifi ba, kuma ba a gabatar da shi a gaban wata kotu ba.

An soma tsare shi ne a kasar Afghanistan a shekarar 2011 bayan da aka zarge shi da cewa ya yi jagorancin wata kungiyar mayaka ta Taliban kuma wai har ya taba saduwa da madugun al-Qaida, Osama Bin Laden.

To amma Aamer ya musanta zargin, ya ce ya je ne Afghanistan da iyalinsa don gudanar da aikin ba da jin kai.

XS
SM
MD
LG