Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An sako wakilin gidan rediyon Muryar Amurka a Habasha


Wakilin Gidan Rediyon Muryar Amurka (VOA) Peter Heinlein

Wakilin gidan Rediyon Amurka da mai yi masa tafinta suna gida yanzu

Wakilin gidan Rediyon Amurka da mai yi masa tafinta suna gida yanzu lami lafiya bayan sakinsu daga gidan kason da aka yi.

Jami’an tsaron Ethiopia ne suka damke wakilin Muryar Amurka suna tuhumarsa da laifin kokarin daukan labarai da rahotannin zanga-zangar da ake yi jiya Juma’a. Yau Asabar aka sako Dan jaridar Muryar Amurka Peter Heinlein daga gidan kaso, kuma yanan nan kalau har ya koma masaukinsa.

Shaidun gani da ido suka ce an kama dan jaridar VOA Heinlein da mai masa tafinta jiya Juma’a lokacin da suka nemi tattaunawa da wasu jiga-jigan shirya zanga-zangar da kungiyoyin Islama keyi bayan Sallar Juma’a, Shima Mai masa tafinta Simegineh Yekoye yana gida tare da iyalinsa bayan ya kwana a gidan Ma’aji.Gidan Rediyon Amurka VOA ya fidda sanarwar cewa yanzu hankali ya kwanta bayan samun labarin sakin wakilin nata da mai masa tafinta daga daurin kwana gudan da hukumomin Ethiopia suka yi masu.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG