Masu binciken na jami’ar ta jihar Florida suna cikin wata kungiya da ake kira Medicines for Malaria Venture da ya kunshi wadansu manyan jami’oi na duniya.
An bayyana cewa a cikin binciken, an samo magani mai suna ELQ-300, wanda za a fara gwadawa a dakin gwaje-gwaje kafin a fara saidawa ga jama’a. An kuma ce maganin, ELQ-300 ya kayatar sosai a wadansu gwaje-gwaje. A cikin bayanin su, masu binciken sun ce maganin zai yi amfani sosai kuma ba zai kai magungunan da suke kasuwa yanzu tsada ba.